Connect with us

Labarai

Rundunar Operation Safe Haven ta kama manyan yan fashi 4

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta Operation Safe Haven, ta kama manyan yan fashi 4 tare da ƙwato bindigu da harsasai a jihar Filato.

 

Jamiʼin yada labaran rundunar Major Samson Nantip Zhakom, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.

 

Sanarwar, ta ruwaito cewa, a sojoji sun kama wasu yan fashi 2 dauke da bindiga kirar Pistol yayin da su ke sintiri a unguwar Naraguta a daren ranar Asabar.

 

Ta kuma kara da cewa, a safiyar Lahadi kuma sun sake kama wani ƙasurgumin ɗan fashi a kusa da Crest Hotel da ke Jos ta Arewa, inda aka same shi da bindiga da harsasai.

 

Bayan bincikarsa ya fallasa abokinsa wanda shi ma tuni an kamo shi a Masallacin Idi na Ali Kazaure.

 

Haka kuma, ta cikin sanarwar, jami’in ya kuma bayyana cewa, binciken ya gano wata bindiga da harsasai a maɓoyarsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!