Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar sojan kasar nan ta ce akalla yan boko haram 32 ne suka mika wuya

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan ta ce akalla mayakan Boko Haram 32 ne suka mika wuya ga jami’an Sojin bayan da suka ajiye makamansu a Jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Texas Chukwu ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, inda ya ce a cikin wadanda suka mika makamansu akwai wani Ibrahim Lawal daya mika bindiga kirar AK47 GUDA.

Janar Texas Chukwu ya kara da cewa Ibrahim Lawal ya kuma mika wasu alburusai guda 59.

Haka zalika ya shaida cewa suna nan suna ci gaba da yi wa wadanda suka ajiye makaman na su tambayoyi kuma da zarar sun kammala za su mika su ga hukumomin da suka kamata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,608 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!