Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin jihar Lagos ta sanya dokar takaita zirga-zirgar manyan motoci

Published

on

Gwamnatin Jihar Lagos ta sanar da sanya dokar takaita zirga-zirgar manyan motocin dakon mai a fadin Jihar, tare da alkawarin ware musu da na su titin da za su rika bi.

Hakan dai ya biyo bayan mummunan hadarin da ya faru a gadar Otedola da ke kan hanyar Lagos zuwa Badin a ranar Alhamis din da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kwamishinan Sufuri na Jihar Ladi Lawanson ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana wanda ya hadar da kungiyar masu dakon mai da iskar gas ta kasa NUPENG, da kungiyar direbobin tanka, da sauransu.

Haka zalika gwamnatin Jihar ta kuma ce duk wani direban tankar da zai shiga birnin wajibi ne ya nemi izini daga ma’aikatar Sufuri ta Jihar kwanaki 30 kafin shigowarsa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,434 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!