Connect with us

Labarai

Rundunar Sojan Najeriya ta bukaci al’umma da kar su tsorata sakamakon harbin Bindiga ranar Talata

Published

on

 

Rundunar sojan Najeriya  mai kula da tsaron fadar shugaban kasa ta umarci al’umma da kada su tsorata lokacin bikin yancin Najeriya da zaa gudanar ranar Talata mai kamawa.

Mataimakin jamiin hulda da jamaa na rundunar sojan Najeriya Haruna Tagwai ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitarwa manema labarai a birnin tarayya dake Abuja.

Yace bikin cikar Najeriya shekaru hamsin da tara zaa gudanar da shi ne a filin fadar shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja, inda suka yi kira ga al’ummar da ke zaune a yankin Asokoro da Maitama a Abuja da su zama cikin shiri.

Haruna Tagwai ya kara da cewa a cikin a al’adar bukukuwan na ranar yancin Najeriya za’a ji harbe harbe da aka saba lokacin bukukuwan na yancin Najeriya.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,922 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!