Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar sojan saman Nijeriya ta fitar da jerin sunayin manyan jami’anta 41

Published

on

Rundunar Sojin saman kasar nan ta fitar da jerin sunayen manyan jami’anta 41 da ta yi wa sauyin wuraren aiki, da suka hadar da masu mukamin Air Vice Marshal 19 da Air Commodores 14 da Group Captain guda 4, sai Wing kwamanda 2 da kuma Squadron Leader 2.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar Air Vice Marshal Olatukunbo Adesanya ya bayar, t ace sauye-sauyen wuraren aikin sun faru ne sakamakon daga likkafar wasu manyan jami’an da aka yi a kwanan nan, tare kuma da tabbatar da gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Daga cikin wadanda sauyin ya shafa akwai Air Vice Marshal Lawal Alao da aka nada a matsayin kwamandan Kwalejin horas da Sojoji da ke Jaji da kuma Air Vice Marshal Mahmoud Ahmad wanda shi ne babban jami’in gudanarwa a shelkwatar Rundunar.

Air Vice Marshal Adesanya ya bayyana cewa ana sa-ran sabbin jami’an Sojin saman fara aiki a sabbin wuraren na su a gobe Talata 2 ga wannan wata na Janairun sabuwar shekarar 2018.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!