Labarai
Rundunar sojin Najeriya sun hallaka jagoran ’yan bindiga Kachalla Kallamu

Rundunar Battaliyan Sojoji na 8 Division a kasar nan sun kashe shahararren jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto kamar yadda Wani majiyar jami’an tsaro ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai ta kasa NAN
Majiyar ta ce Kallamu, wanda shakiki ne ga shahararren jagoran ’yan bindiga, Bello Turji, an kashe shi ne tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai a yankin, a wani samame na musamman da sojojin Nigeria Army suka gudanar a ƙauyen Karawa da safiyar ranar Litinin.
Rahoton ya kara da cewa Kallamu, wanda ya fito daga Garin-Idi a Sabon Birni, ya jima yana addabar al’ummomin yankin, kuma kwanan nan ya dawo daga jihar Kogi bayan ya gudu sakamakon farmakin sojoji a watan Yuni 2025, inda aka ce ya nemi mafaka.
Mai ba Gwamnan Jihar shawar kan tsaro kanal Ahmad Usman mai ritaya, da wasu mazauna jihar sun yabawa Sojojin Najeriya kan nasarorin da suka samu a yaki da ’yan bindigar.
You must be logged in to post a comment Login