Labarai
Rundunar Sojin Najeriya sun hallaka ‘yan ta’adda a Jihar Borno

Dakarun Sojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda shida tare da dakile yunkurin kai hari garin Malam Fatori da ke Jihar Borno, inda suka kwato manyan bindigogi kirar AK-47 guda biyar, harsasai sama da 250, da wasu bama-bamai da kuma sauran makamai.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar a ranar Talata, aka kuma rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan sun kai hari sansanin sojoji, amma dakarun hadin gwiwa da karin sojoji daga shiyoyi uku suka fatattake su
You must be logged in to post a comment Login