Labarai
Rundunar Sojin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar dakaru 17 a musayar watar da suka yi da yan bindiga

Rundunar Sojin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar dakarunta 17 yayin da wasu kuma suka samu raunika a wata musayar wuta tsakanin sojojin da kuma ‘yan bindiga a ranar Talata a Kwanan-Dutse da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.
‘Yan Bindigan sun farmaki sansanin sojojin da ke yankin Kwanan-Dutse mai tazara kadan daga Bangi, shalkwatar karamar hukumar Mariga.
Rundunar Sojin ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa, akwai yiyuwar samun karuwar wadanda suka mutu tsakanin sojojin da kuma yan bindigar.
Shugaban karamar hukumar Mariga Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya ce harin ya kara saka tsoro da fargaba ga manoman yankin.
You must be logged in to post a comment Login