Labarai
Rundunar Sojin Najeriya ta yabawa dakarunta bisa dakile harin ‘yan ta’adda a Jihar Kano

Babban kwamandan sojojin Najeriya na runduna ta daya sashen Operation Fansar Yamma Manjo Janar Abubakar Wase, ya yabawa dakarun sojin bisa yadda suka nuna kwarewa da jajircewa wajen dakile harin ‘yan ta’adda a Karamar Hukumar Shanono dake jihar Kano.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mataimakin mai magana da yawun rundunar Caftin Babatunde Zubairu ya rabawa manema labari bayan ziyarar da rundunar ta kai yankin Farin Ruwa da Tsaure na garin Shanono a Jihar Kano.
Sanarwar ta ce, babban kwamandan yayi kira ga dakarun nata da su ci gaba da jajircewa wajen ganin suna aikinsu yadda ya kamata, don ganin sun yaki ta’addanci a Jihar Kano.
Haka zalika sanarwar ta ce duba da yankin Shanono yana tsakanin Bodar Kano da Katsina da ke Arewacin Najeria, ya sanya wurin ya zama yankin da ‘yan ta’adda suke addaba a yanzu, don haka yake kira ga dakarun da su sanya idanu sosai, da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro don yakar matsalar.
You must be logged in to post a comment Login