Labarai
Rundunar soji a Najeriya sun kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a jihar Kogi

Dakarun runduna ta 12 ta sojojin kasar nan sun fatattaki ‘yan bindiga tare da kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a hanyar Oshokoshoko zuwa Obajana a karamar hukumar Lokoja a jihar Kogi.
Wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin ta 12 Laftanar Hassan Abdulahi ya fitar a safiyar yau Laraba, ta ce, farmakin na daga cikin kokarin da ake yi na yaki da ‘yan fashi masu garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka a fadin jihar.
Ya ce, a safiyar jiya Talata ne dakarun suka kai farmakin bayan sahihan bayanai kan yadda ‘yan bindiga suka sace wasu mutane tare da tserewa da su a kan titin Oshokoshoko zuwa Obajana inda nan take dakarun sojin da ke sansanin sintiri na Kabba, tare da hadin gwiwar wasu rundunonin hadaka, suka gudanar da wani samame na musamman domin kame bata garin.
Haka kuma, ya kara da cewa, yayin harin an kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da kuma ceto wani da aka yi garkuwa da shi
You must be logged in to post a comment Login