Labarai
Rundunar yan sadan jihar Kaduna ta sha alwashin kare rayuka da dukiyar al’ummar Kajuru
Rundunar yan sadan jihar Kaduna ta sha alwashin kare rayuka da dukiyar al’ummar Kajuru.
Rundunar yan sadan jihar Kaduna ta sha alwashin kare rayuka da dukiyar al’ummar Kajuru da ke jihar bayan da ‘yan ta’adda suka hallaka a kalla mutane 130 a yankin a baya-bayan nan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kaduna Ahmad Abdurrahman ne ya bayar da tabbacin inda ya ce za a bi musu hakkin su kamar kowanne dan Adam.
Yayin zantawar sa da manema labarai kwamishinan yan sandan ya ce rundunar yan sandan jahar na gudanar da binciken kwakkwafi domin gano gaskiyar lamarin.
Ya kuma ce kawo Yanzu haka rundunar ta kama mutane da dama da ake zargin suna da hannu a cikin al’amarin, inda ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin masu hannu a cikin sun girbi abin da suka shuka.
Ya kuma ce ba lallai ne adadin da gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufa’I ya ce sun mutu a yankin su kasance haka ba, a cewar sa za su iya karuwa ko raguwa, tunda dai bai gudanar da binicike ba.