Labarai
Rundunar ‘yan sanda ta tura Jami’ai kasuwanni da kan iyakoki a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta ce ta ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa tsaro domin daƙile ayyukan ‘yan bindiga da sauran laifuka a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sani Omolori Aliyu, ya bayyana cewa sun ƙara tura jami’ai a kasuwanni, tashoshin mota da kuma yankunan kan iyaka domin tattara bayanan sirri da kuma ɗaukar matakan tsaro kafin aukuwar laifi.
Wannan matakin dai ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya bayar na mayar da hankali kan aikin ‘yan sanda na zamani da zai dogara kan bayanan sirri a faɗin ƙasar nan
Haka kuma rundunar ta ce tana ƙara kusantar al’umma ta hanyar tarurruka da kuma wayar da kan jama’a kan yadda za su gane barazana da kuma hanyoyin neman agajin gaggawa.
You must be logged in to post a comment Login