Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi zagaye wuraren da ake aikata laifuka

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi zagaye wuraren da ake gudanar da ayyukan bata gari da rashin tsaro suka kamari.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Muhammad Wakili ne ya bayyana hakan yayin zagayen duba maboyar bata gari a yankunan Badawa da Giginyu dake karamar hukumar Nassarawa.

Ya ce rundunar ‘yan sandan jihar Kano tuni ta fito da hanyoyin da zata tsaftace yankunan daga ayyukan bata gari da shan kwayoyi.

Da yake jawabi, jagoran al’ummar yankin Badawa Malam Muhammad Ibrahim Makkawi yace sun jima suna fama da ayyukan masu shaye-shaye miyagun kwayoyi da sauran laifuka.

Al’ummar yankin Badawa dai sun yi kira ga Gwamnati da ta duba yiwuwar gyara musu konanniyar makarantar ‘yan mata ta Badawa duba da koma bayan da rashin gyaran ke iya haifarwa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,758 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!