Labarai
Rundunar ‘yan sandan Kano ta yi tattakin Kilomita 10 don tabbatar da tsaro
Rundunar ƴan sandan jihar Kano tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun gudanar da tattaki na tsawon kilomita 10 a shirye-shiryen su na bayar da tsaro a lokacin bukukuwan babbar sallah bana da ke tafe.
An fara gudanar da tattakin ne daga filin wasa na Sani Abacha da ke unguwa Ƙofar Mata da misalin ƙarfe 6:00 na safe, inda aka yi tafiyar ƙafa zuwa ƙananan hukumomi 3 da suka haɗa da Dala, Gwale da kuma ƙaramar hukumar birnin Kano.
Da yake bayyana makasudin tattakin, kwamishinan yan sandan jihar Muhammad Usaini Gumel, ya ce, an kirkire shi ne domin wayar kan al’umma muhimmancin zaman lafiya tare da yin jan kunne ga masu son tada fitina.
Haka kuma, Kwamishinan ‘yan sandan, ya bukaci hadin kan mazauna jihar Kano da su tabbatar da cewa sun gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana.
Rahoton: Aminu Abdu baka Noma
You must be logged in to post a comment Login