Labarai
Rundunar yan sanda ta bada umarnin janye jami’anta daga kare manyan mutane

Babban Sufeton ‘yan sandan kasar nan Kayode Egbetokun, ya ba da umarnin janye jami’an ‘yan sandan ko ta kwana na kwantar da tarzoma wato MOPOL daga kare manyan mutane (VIPs). kamar yadda aka sanar a shafin rundunar na X.
Shafin X, na rundunar ya tabbatar dacewa Kayode Egbetokun ya bayyana haka ne a hedikwatar rundunar da ke birnin tarayya Abuja yayin wata ganawar gaggawa da ya yi da kwamandojin rundunar ta Mopol.
Ganawar ta biyo bayan cece-kucen da ya barke kan wani faifan bidiyo da ya nuna wani dan kasar China yana ba jami’an na Mopol kudi a bainar jama’a, da hakan ya sa rundunar ta gayyaci jami’an da aka gani a bidiyon domin amsa tambayoyi, da ya ce an ɗauki matakin ladabtarwa a kansu.
Kayode Egbetokun, ya nuna rashin jin dadin sa tare da sukar kwamandojin rundunar ‘yan sandan ta MOPOL, bisa yadda suke tura jami’an sashen zuwa tsaron manyan mutane a kasar.
You must be logged in to post a comment Login