Connect with us

Labarai

Rundunar ‘yan-sandan Najeriya ta tura dakarunta Jihar Benue domin dakile rikice-rikcen Jihar

Published

on

Rundunar ‘yan-sandan Najeriya ta tura dakarunta kwararru na musamman da aka raba zuwa rukunoni 15 zuwa Jihar Benue domin dakile rikice-rikcen da ke faruwa a Jihar.

Kwamishinan ‘yan-sandan Jihar ta Benue Fatai Owoseni ya bayyana cewa Babban Sufeton ‘yan-sandan kasar nan Ibrahim Idris ne ya bada umarnin girke jami’an, inda ya sanar da cewa sun ceto wani jami’insu da ya yi batan dabo lokacin da aka kai hari a  kananan hukumomin Yogbo da Guma a Jihar.

Ya kara da cewa an rarraba jami’an a yankunan Kwande da Agatu da Makurdi da Buruku da Katsina-Ala da Gwer ta Yamma da kua Vandeikya.

Haka zalika ya shaida cewa jami’an na su sun zamu zarafin fatattakar masu kai hare-haren inda zaman alfiya ya fara samuwa a Jihar Benue.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!