Labarai
Rusau: Abba Gida-gida zai daukaka ƙara kan biyan diyyar biliyan 30
Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na biyan diyyar Naira biliyan 30 sakamakon rushe filin Idi da ke cikin birni.
Kwamishinan shari’a na jihar Barr. Haruna Isa Dederi ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan yanke hukuncin.
Ya ce, gwamnati za ta yi amfani da ‘yancinta na ɗaukaka ƙara gaban kotun ɗaukaka ƙara don soke hukuncin.
“Kada ku manta cewa idan wani ya yanke shawarar neman haƙƙinsa a gaban kotu, kuma ya samu hukuncin da ya dace, hakan ba yana nufin ƙarshen shari’ar kenan ba, domin kuwa akwai kotun ɗaukaka ƙara”
‘’Kuma tun da farko mun sanar da kotun cewa ba ta da hurumin sauraren ƙarar, amma ta ci gaba da yi har aka zo ta yanke hukuncin”
A ranar Juma’a ne babbar kotun tarayya da ke Kano ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta biya diyyar Naira biliyan 30 ga waɗanda rusau ɗin masallacin Idi ya shafa,domin kuwa an ruguje shagunan ba bisa ka’ida ba.
You must be logged in to post a comment Login