Connect with us

Labarai

Sai da binciken kwakwaf za’a shawo kan matsalar cin hanci -Anas Aremauyaw

Published

on

Aikin jarida na binciken kwa-kwaf wani babban makami ne wajen yake da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Kwararren dan jaridar nan kuma wanda ya karbi kyaututtuka da dama kan kwarewar sa dan asalin kasar Ghana  Anas Aremayaw ya ce, aikin jarida na binciken kwa-kwaf wani babban makami ne wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Haka zalika Anas yace rahoton bincikar kwa-kwaf wani makami ne na yaki tare da shawo kan matsalolin cin hanci da rashawa a kasar nan, da ma nahiyar Afrika baki daya.

Anas Aremeyew ya bayyana hakan ne a yayin bude taron karawa juna sani na kwanaki biyu ga masu aikin jarida na binciken kwa-kwaf na nan gida Najeriya da kuma kasar Ghana da malamai da dalibai masu nazari a jami’o’I da kwalejojin ilimi da kimiyya da fasaha wanda aka yi a harabar jami’ar Bayero dake nan Kano a yau Alhamis.

Da yake jawabi kan yadda yake tattara bayanai wajen hada rahoton fallasa ko bankada masu cin hanci da rashawa, Anas yace akwai kalubale daban-daban da yake fuskanta, amma hakan bai kashe masa gwiwa ba, a don haka ya bukaci ‘yan jarida da dalibai masu nazari da su dinga bincikar kwakwaf wajen yin rahotannin kwarmata masu cin hanci da rashawa a cikin alumma.

 

A yayin da dalibai ke masa tambayoyi kan yadda yake rufe fuskar sa don kada a gane shi a cikin alumma, dan jaridar ya ce wata alama ce da yake amfani da shi don kare kan sa, yayin da ya bukaci makarantu da jami’o’I a kasashen Afrika da su sanya nazari kan ilimin binciken kwa-kwaf na jarida a tsarin manhajar su, a wani mataki na karfafawa dalibai yin rahoton bincike kan cin hanci da rashawa.

Da yake jawabi fitaccen dan jaridar nan kuma tsohon babban sakatare  a ma’aikatar yada labarai, Ahmad Aminu yace yawancin ‘yan jaridar yanzu sun sanya tsoro a zukantan su, a don haka ya bukace su da su sake jajircewa wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata, mussaman ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,958 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!