Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan bindiga dadi sunyi garkuwa da mutane 8 a jihar Kaduna

Published

on

Wasu yan bindiga dadi sun yi garkuwa da wasu malami guda biyu da dalibai 6 dake makarantar Engraver a Kakau a garin Daji da ke cikin karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna .

 

Mai Magana da yawun bakin rundunar yan sanda jihar kaduna ne ya bayyanawa jaridar  DailyNigeria , faruwar hakan, tare da cewar tuni ake yunkurin hanyoyin da za’a kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

 

Daya daga cikin iyayen wanda aka yi garkuwan da su, ya bayyanawa jaridar Thecable,cewar ya samu waya daga  wadanda suka yi garkuwar a safiyar yau.

 

Ya kara da cewa sun sami lambar wayar ta sa ne a hanyar ‘yar ta sa, a lokacin ne ya gane cewar an sace ‘yar ta sa, ya kara da cewa ya kasa fahimtar wayar da suka yi ko suna bukatar kudi ne, saboda suna wani yare da baya fahimta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!