Labarai
Saka hannun jari: Buhari zai tafi Riyadh babban birnin Saudi Arebiya
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Riyadh na kasar Saudiyya aa ranar Litinin 25 ga Oktoba.
Tafiyar ta shugaba Buhari wani ɓangare ne halartar taron saka hannun jari na manyan kamfanoni daga Najeriya, da masu bankuna, manyan masana’antu da ƙwararrun masana makamashi don tattauna batutuwan da suka shafi makomar saka hannun jari a fadin duniya.
Taron wanda shi ne karo na 5 za a shafe kwanaki uku ana gudanar da shi kuma zai karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen duniya da dama.
Shugaba Buhari zai gudanar da aikin Umrah gabanin dawowarsa gida Najeriya a ranar Juma’a.
Ana sa ran shugaba Buhari zai samu rakiyar ministan sadarwa da tattalin arziki Dakta Isa Ibrahim Pantami da ƙaramin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada, da karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva.
Sauran sune: mashawarcin shugaban ƙasa kan sha’anin tsaro Manjo janar Babagana Monguno, da shugaban hukumar Leken asiri ta ƙasa ambasa Ahmed Rufa’i Abubakar da shugaban hukumar kula da zuba Jari Uche Orji sai shugaban hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙetare Abike Dabiri-Erewa.
Ƴan kasuwar da ake sa ran halartar su taron sun haɗa da Alhaji Mohammed Indimi, Alhaji Aliko Dangote, Tope Shonubi, Wale Tinubu, Alhaji Abdulsamad Rabiu, Hassan Usman, Omoboyode Olusanya, Abubakar Suleiman, Herbert Wigwe da Leo Stan Ekeh.
Garba Shehu.
You must be logged in to post a comment Login