Siyasa
sama da jam’iyyun siyasa 100 ne za su shiga takara a zaben shekarar 2019-inec
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce sama da jam’iyyun siyasa dari ne za su fito cikin takardar kada kuri’a a yayin babban zaben shekarar 2019.
Shugaban hukumar na kasa Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan Alhamis din nan, lokacin da yake jawabi yayin taron masu ruwa da tsaki kan al’amuran zabe wanda aka gudanar a Abuja.
Taron wanda hukumar ta INEC ta shirya tare da hadin gwiwar wata kungiya da ke sanya ido kan al’amuran zabe da hukumar DFID, an gudanar da shi ne karkashin inuwar kungiyar da ke rajin isar da sako ka jama’a kan sha’anin zabe.
Farfesa Mahmood Yakubu ya lura da cewa kungiyoyin siyasa dari da talatin da takwas ne suka yi rijista a matsayin jam’iyyun siyasa, karkashin hukumar ta INEC.
A cewar sa an tura jami’an hukumar lura da shige da fice ta kasa dukkanin cibiyoyin da ake gudanar da rajistar katin zabe a fadin kasar nan, wanda har hakan ta sanya aka samu nasarar gano wadanda ba ‘yan asalin kasar nan ba, da yunkurin yin rajistar katin na zabe.
Shugaban hukumar ta INEC ya bayyana cewa hukumar bata da ikon hana kungiyoyin siyasa rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.