Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Siyasa

Bukola Saraki ya kalubalanci sabon shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole da sauran sabbin shugabannin jam’iyyar

Published

on

Shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki ya kalubalanci sabon shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole da sauran wadanda aka zaba tare da shi da su gudanar da ayyukan su cikin gaskiya da rikon amana.

Sarki ya yi wannan kira ne lokacin da ake kammala taron jam’iyyar APC na kasa da aka kammala jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja.

Ya kuma ce a wannan lokaci da jam’iyyar ke neman makoma mai kyau a nan gaba, akwai bukatar sabbin shugabannin su waiwayi rawar da suka taka a shekarar 2015 su kuma tuna yadda suka murkushe jam’iyyar PDP a wancan lokacin domin dorawa a gaba.

Bukola Saraki ya kuma ce ya lura akwai wasu muhimman mutane da basu halarci taron ba inda ya ce akwai bukatar a bisu a lallaba su akuma yi tafiyar tare da kowa da kowa.

Ya kuma ce jam’iyyar ya kamata ta tuna nasarar da tayi baya, adon haka jam’iyyar ta dunkule wuri guda domin sake samun irin wanan nasar da ta samu a baya.

Ko da yake Sarakin ya ce ya amince a kwai matsalolin da ba za a rasa ba a cikin jam’iyyar inda ya ce wanan kuma alhakin sabbin shugabannin ne suga cewar sun dawo da komai kan tsari.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!