Labarai
Samar da ilimin addini zai gyaran zamantakewa- Gwamnan Kano
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci buɗe cibiyar bincike kan addinin Musulunci da koyar da karatun Alqur’ani mai girma wadda aka yiwa laƙabi da Musa Sale Maji dadi domin ƙara bunƙasa harkar ilimin addinin Musulunci a faɗin jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ‘samar da ilimin addini ga al’umma zai taimaka wajen samar da ilimin zamantakewa da yin koyi da ɗabi’un ma’aiki SWA’.
Gwamnan yayi wannan jawabin ne yayin da ƙaddamar da buɗe cibiyar dake Miller Road a yau Asabar.
A nasa bangaren jagoran cibiyar tsohon sanatan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ‘wannan Cibiyar matasan da zasu amfana da wannan Cibiyar sun fara daga shekaru 15 zuwa 25, wadanda zasuyi karatu tun daga Firamare har zuwa gaba’ da sakandire, da gwamnati zata dauki nauyinsu’.
Freedom Radio ta rawaito cewa gwamnatin Kano tace zata dauki nauyin cibiyar domin yin karatu batare da biyan kuɗi ba.
You must be logged in to post a comment Login