Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hadin kan Gwamnatin tarayyar ga manoma zai bunkasa noma- Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga gwamnatin tarayya kan ta bai wa manoma hadin kai wajen samar musu kayayyakin noma na zamani  domin samar da wadataccen abinci a Nijeriya.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara gidan gonar Malam Alu da ke birnin kudu ta jihar Jigawa.

Sarkin ya ce, gidan gonar Babu irinsa a arewacin Nijeriya duba da irin noman Tumatir da kiwon shanu da kaji da kuma samar da Madarar Shanu mai inganci da ake yi a gonar.

A nasa jawabin mai martaba sarkin Dutse Alhaji Muhammadu Hamim Nuhu Sunusi ya ce, ‘sun ji dadin wannan ziyara da sarkin kano ya kai musu.

Mai martaba sarkin kano yayin ziyarar ya na tare da hakimansa.

 

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!