Labarai
Samar da jami’o’i masu zaman kansu a Arewa ya kawo ci gaba a fannin ilimi – Amanallah Ahmad
Mai fashin baƙi kan al’amuran yau da kullum Alhaji Amanallah Ahmad Muhammad ya ce, samar da jami’o’i masu zaman kansu zai rage fitar ɗalibai zuwa ƙasashen ƙetare domin neman ilimi.
Amanallah Ahmad ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom radio.
Yana mai cewa, samar da jami’o’in zai rage jinkirin da ɗalibai ke samu saboda yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’o’i ke tafiya saboda buƙatunsu.
“Shigowar jami’o’i masu zaman kansu Arewacin ƙasar nan ya kawo ci gaba a fannin ilimi, sannan zai rage kunkoson da ake samu a jami’o’i da kuma rashin samun guraben karatun ga wasu ɗaliban.”
“Jami’o’i masu zaman kansu na da tasiri wajen bai wa ɗalibai damar samun ƙwarewa a fannin kimiyya da fasaha.”
Amanallah ya zargi cewa gwamnatocin Arewacin Najeriya sun yiwa ɓangaren ilimi riƙon sakainar kashi shi yasa yabkin kudancin Najeriya suka yiwa yan Arewa fintinkau.
You must be logged in to post a comment Login