Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Siyasar Kano: Rikici na neman sake kunnowa a Kwankwasiyya

Published

on

Ana raɗe-raɗin wani rikicin cikin gida na shirin ɓarkewa a jam’iyyar PDP Kwankwasiyya, tsakanin manyan jiga-jiganta biyu.
Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-gida, tsohon Kwamishinan ayyuka na jihar Kano, kuma ɗan takarar Gwamnan jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019.

Sai kuma Dr. Adamu Yunusa Ɗangwani tsohon Kwamishinan ruwa, kuma tsohon shugaban maa’aikatan fadar Gwamnatin Kano.

Dambarwa ba ta rasa nasaba da kiraye-kirayen da magoya bayan Ɗangwanin ke yi na ya fito takarar Gwamna, abin da kuma bai yiwa masu bin Abba Kabir daɗi ba.

Me ke faruwa a tsakanin ɓanagrorin biyu?
Rahotannin da Freedom Radio ta tattara sun nuna cewa, tsamin dangantakarsu ta soma fitowa fili ne a ranar Alhami 2 ga watan Disambar da muke ciki.
A lokacin da tawagar magoya bayan Sanata Kwankwaso suka taro shi daga filin jirgin sama, sannan suka wuce ta’aziyya gidan Alhaji Yusuf Fantiya, da kuma gidan marigayi Alhaji Sani Buhari Daura.
Sai dai bayan da aka dawo gidan tsohon Gwamnan da ke Miller Road, an zargi wasu magoya bayan Abba Gida-gida da yiwa Ɗangwani ihun “Kano Sai Abba”.

Washegari Jumu’a 3 ga watan, sai ba a ga Ɗangwani ya bi tawagar Sanata Kwankwaso ta zuwa garin Ɗanbatta domin jana’izar marigayi Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan.
Maimakon hakan shi ma tawagarsa daban ta je ta yi ta’aziyya a Ɗanbatta.

Hoton ziyarar su Dr. Yunusa Ɗangwani a gidan Alhaji Atiku Abubakar

A ranar Talata 7 ga watan Disambar dai Dr. Ɗangwani da tsohon Kwamishinan kuɗi Yusuf Bello Ɗanbatta da kuma tsohon ɗan majalisar tarayya Abubakar Nuhu Ɗanburan suka gana da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.
A cikin wannan hoto da aka yaɗa, ya nuna Ɗangwani baya sanye da jar hula, abin da ba a saba gani ba.

Dr. Adamu Yunusa Ɗangwani da Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso

Ɗangwani yana takarar Gwamna?
Magoya bayan Dr. Adamu Yunusa Ɗangwani suna ta yin kiraye-kiraye musamman a kafafen sada zumunta kan ya fito ya yi takarar Gwamnan Kano.
Lamarin da ke samun suka daga magoya bayan Abba gida-gida waɗanda suke ganin hakan tamkar yin tawaye ne ga madugunsu Sanata Kwankwaso.

Meye matsayar Abba gida-gida a kai?
Game da musayar yawun da ake ta gwabzawa tsakanin magoya bayan ɓangarorin a shafukan sada zumunta, mun tuntuɓi mai taimakawa Abba Kabir Yusuf kan kafafen Ibrahim Adam sai dai ya ce, ba zai ce komai ba a kai.

Ina matsayar Ɗangwani?
Mun so ji daga bakin Dr. Adamu Yunusa Ɗangwani sai dai haƙanmu bai cimma ruwa ba, amma wani makusancinsa da ya nemi a sakaye sunansa ya yi mana ƙarin haske a kai.

Ya ce “Dr. Ɗangwani bai taɓa cewa zai fito takara ba, mu ne muka ga dacewar hakan muke kiransa da ya fito”.
“Kuma tafiya zuwa Ɗanbatta lokacin da aka sanar da shi a ƙurace ne, kafin ya fito tawaga ta tafi shi yasa ya je daga baya”

Ya ci gaba da cewa “Akwai zuwa ta’aziyyar Alhaji Sani Gote ma da bai samu zuwa ba, sabota ita ma an sanar da shi a ƙurace kuma a lokacin yana Albasu”.

Dangane da ziyarar gidan Atiku Abubakar kuwa ya shaida mana cewa, tawagar su Dr. Ɗangwani ta je gidan Sanata Abdul Ningi a Abuja domin yi masa ta’aziyya amma sai suka iske ya tafi gidan Atiku shi ne suka je can.
Kuma babu wata tattaunawa da aka yi game da siyasar Kano.

Koda muka tambaye shi cewa, shin ya taɓa tsawatar musu kan kiraye-kirayen da suke masa ya fito takara? Sai ya ce ai kowane mutum yana da ƴancin fitowa a dama da shi.

A nata ɓangaren jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta ce, ba ta da masaniya game da batun wannan dambarwa.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Bashir Sanata ya ce, zai sanar damu da zarar ya samu ƙarin bayani a kai.

Ku kalli wasu daga cikin saƙonnin da wasu mabiya ɓangarorin suka wallafa a shafukansu na Facebook kan wannan batu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!