Connect with us

Labarai

Sanata Rabi’u Kwankwaso ya dage ziyararsa zuwa Kano

Published

on

Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya dage ziyarar da yayi shirin kawo wa nan Kano.

Da ya ke jawabi tsohon Sakataren gwamnatin jihar Kano Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana cewa sanata Kwankwaso ya janye kawo ziyarar tasa ne sakamakon tun tubar wadanda abin ya shafa.

Sanata Kwankwaso ya kuma kara da cewa a dage kawo ziyarar tasa ne don gujewa samun hargitsi da tashin hankali yayin ziyarar, biyo bayan shawarwari daga gurare daban-daban.

Sanata Kwankwaso ya kuma baiwa Al’ummar Jihar Kano Hakurin dage ziyarar tasa yana mai cewa hakan ya zama dole don kare rayukan al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,434 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!