Connect with us

Labarai

Sarkin Kano ya dakatar da mai Unguwar Badawa

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya dakatar da mai Unguwar Badawa bakin Kwangiri daga aikinsa na mai Unguwa, a sakamakon goyon bayan dansa Hamza babaye wajen aikata ta’addancin dabanci a yankin cikin karamar hukumar Nassarawa.

Muhammadu Sunusi II ya bayyana hakan ne yayin da ake gabatar masa da rahoton irin ta’addancin da Hamza Babayo dan mai Unguwar yake gudanarwa da hakimin Nassarawa ta hannun wakilinsa ya gabatar a fada.

An gabatarwa da sarkin Kano irin yawan mutanan da Hamza dan mai Unguwa ya lahanta wadanda a halin yanzu wasu sun samu nakasa, wasu kuma suna asibiti.

Malam Muhammadu Sunusi II ya ce, masarautarsa baza ta amince da daurewa matasa da ‘Ya ‘Yan wanda suke rike da mukaman sarauta gindi ba, wajen aikata ta’addanci, sannan ya bada Umarni ga Hakimin Nassarawa da ya zurfafa bincike akan zargin da ake yiwa mai Unguwar Badawa kwangiri domin tabbatar da laifin .

Al’ummar yankin dai sun gabatar da korafe korafe daban-daban akan dakattacen mai Unguwar ta Badawa Kwangiri tare da gabatar masa da wadanda dan mai Unguwa ya raunana a yankin da makamai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,480 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!