Connect with us

Labarai

Sarkin Kano ya bukaci sarakunan kofofin Kano su himmatu wajen samar da zaman lafiya

Published

on

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga sarakunan kofofin Kano, da su himmatu wajen ganin an samar da zaman lafiya da kare mutuncin al’umma da addinin a yankunan su.

Muhammadu Sanusi II ya yi wannan kira ne lokacin da yake tabbatar da sarkin kofar Gadon-Kaya Alhaji Bello Isa Idris a matsayin sabon sarkin kofar ta Gadon kaya dake karamar hukumar Gwale.

Sarkin ya kuma bayyana cewa sarakunan kofofin suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ganin an samu dai-daito da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan su.

Jim kadan bayan kammala Nadin nasa a matsayin sabon Sarkin kofar Gadon-Kayan wanda ya gaji mahaifin sa Alhaji Isa Idris ya sha alwashin kare kima da martabar mukamin da aka nada shi da kuma ta masarautar Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,608 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!