Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

CBN ya yanke shawarar hukunta kamfanin MTN da wasu bankunan kasuwanci

Published

on

Babban bankin kasa CBN ya ce ya yanke shawarar hukunta kamfanin sadarwa na MTN da kuma wasu bankunan kasuwancin kasar nan hudu sakamako saba ka’idar fitar da kudade ketare da suka yi.

Bankunan kasuwancin sun hadar da bankin standard chartered, da kuma stanbic IBTC da Citibank sai kuma Diamond inda babban bankin  na CBN ya zarge su da tallafa wa kamfanin na MTN wajen fitar da kudaden.

Gwamnan babban bankin CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai da yammacin jiya Litinin a kasar china.

Gwamnan ya ce ya na so ya fayyace wa al’ummar Najeriya halin da ake ciki duba da cewa laifin da kamfanin na MTN da kuma bankunan suka aikata na da girman gaske wanda kuma ya ja hankalin al’ummar duniya baki daya.

Ya kuma ce idan kamfanin na MTN ya dawo da kudaden da ya futar da suka kai dalar Amurka biliyan 8 da miliyan 14, to babban bankin zai karba ya kuma musanya musu da naira da ta yi dai-dai da adadin kudaden da suka fitar.

Ya kuma ce a yanzu haka babban bankin na CBN yana ci-gaba da gudanar da binciken sa kan tuhumce-tuhumce guda uku da ake yi wa bankunan da kuma kamfanin na MTN da kuma yadda suka fitar da kudin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!