Labarai
Sarki Muhammadu Sanusi II ya nada Sarkin Hausawan Turai
Sarki Muhammadu Sanusi II ya nada Sarkin Hausawan Turai
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu ya nada Dakta Surajo Jankado Labbo a matsayin Sarkin Hausawa na kasashen Turai a wani taron bikin Hausawa da aka gudanar a birnin Paris a makon da ya gabata.
Wannan shine karo na farko da sarkin Kano ya gudanar da zama a kasar waje, tare da shirya masa zaman fada cike da kaloli irin na gargajiya, da Hausawa mazauna kasar waje suka hallara a fadar ta sa.
Jaridar Daily Nigeria dai ta rawaito cewar a yayin zaman ne dai aka zabi Dakta Labbo a matsayin sarkin Hausawan mazauna kasar Turai, daga cikin wadanda suka halarci fadar sarkin a birnin Paris dai, sun hadar da gwamna Palaiseau, Gregoire de Lasteyrie.
Sarkin Kano dai ya sauka ne a Turai bayan da ya hallarci taron majalisar dinkin duniya karo na 74 da aka gudanar a birnin New York.
Sarkin dai na fuskantar kalubale da dama a nan gida da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, sai dai na samun girmamawa a idon duniya.