Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Sarkin Musulmi ga Buhari da gwamnoni: Ku gaggauta kawo ƙarshen zubar da jinin jama’a

Published

on

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnonin ƙasar nan da su yi duk me yiwuwa don kawo ƙarshen zubar da jinin jama’a babu gaira babu dalili da ke faruwa a sassa daban-daban na Najeriya.

 

Sarkin na musulmi yayi wannan kiran ne jim kadan bayan kammala sallar idi jiya a Sokoto.

 

Ya ce: “Muna kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kafatanin gwamnonin ƙasar nan da su yi duk me yiwuwa wajen ganin sun magance matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar  nan’’

 

‘‘A matsayin ku na shugabannin mu wajibi ne ku zage dantse ku jajirce don ganin wannan matsala ta zo ƙarshe’’ acewar sarkin musulmin.

Sarkin na musulmi ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su yi addu’oi ga shugabannin su wanda hakan zai taimaka musu wajen daƙile matsalolin da ke damun ƙasar nan a wannan lokaci.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!