Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin musulmi ya bukaci gwamnatin tarayya ta zage dantse don magance matsalolin tsaro

Published

on

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara zage dantse wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi Jihar Zamfara, da wasu sassan kasar nan.

Sarkin musulmin ya yi wannan kira ne yayin ziyarar Sallah da ya kaiwa gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a karshen makon jiya, yana mai kokawa kan adadin mutanen da aka kashe a baya-bayan nan.

Ya kara da cewa duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi, ya zama wajibi su ninka kokarin na su don kawo karshen zubar da jinin al’umma ba gaira-ba saba.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya shawrci jama’a su dage wajen addu’o’in nemawa kasar nan zaman lafiya a kwanciyar hankali a ko bangare na kasar nan

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!