Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Sarkin musulmi ya bukaci shugabanin mabiya addinin kirista su rika duba na tsanaki kafin yin kalaman karfafa gwiwar yan ta’adda

Published

on

Mai alfarmasarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga shugabanin mabiya addinin kirista da su rika yin duba na tsanaki kafin yin kalaman da zasu karfafa gwiwar yan ta’adda a kasar nan.

Sarkin musulmi ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga shugabanin addinai, da jami’an tsaro da ma’iakatan yada labarai da kuma sauran al’umma lokacin da ake taron shan ruwa a jiya Litinin.

Ya kuma dangantabayanan da wasu kafafen yada labarai a kasar nan ke wallafawa wadanda ake danganta su da wasu shugabannin addinin kirista a kasar nan da ke cewa matukar daliba Leah Sharibu ta mutu a hannun mayakan boko haram to kuwa za’a samu rikicin addinin a kasar nan a matsayin abin da bai kamata ba.

Ya ce idan aka yi duba sosai mayakan boko haram sun sace yan mata musulmai wadanda suka mutu a hannun su amma babu wani matakin yaki da al’ummar musulmai suka dauka, inda ya ce ko tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tabbatar da hakan.

Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakarna uku da ya tabbatar da cewa yana Magana ne da yawun al’ummar musulmi, ya yi kira ga ma’aikatan yada labara da su yi kokari wajen ceto kasar nan daga fadawa rikicin addini, inda ya kara da cewa wasu daga cikin rahotannin da suke yadawa na taka rawa wajen rura wutar kiyayya tsakanin al’ummar kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!