Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Zazzau ya fashe da kuka ya yin nadin sa a Zariya

Published

on

A yau Litinin 9 ga watan Nuwamba aka yi bikin bada sandar girma ga sabon Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a birnin Zariya.

Da yake jawabi sabon sarkin Zazzau ya fashe da kuka yana mia cewa ya godewa Allah da gwamantin jihar Kaduna kan wannan nadi da aka yi masa a matsayi sarki na 19

Yana mai cewa “ya gaji kakan sa Malam Musa da ya fito daga gidan Mallawa wanda ya karbo tuta daga  Shehu Usman Dan Fodiyo”.

Bisa al’ada wajibi ne bayan an zabe sarki kuma gwamnati ta tabbatar da shi  sai an yi bikin bada sandar girma ga sabon sarki.

A dai makon da ya gabata ne wata babbar Kotu a jihar Kaduna ta ce ba zata amince da buƙatar da aka shigar gabanta ta neman dakatar da nadin  sabon sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sarki na sha tara a majalisar masarauta.

Iyan Zazzau  Alhaji Bashir Aminu ya shigar da karar a Babbar Kotun jihar Kaduna wacce take zama a Sabon Garin Zariya yana kalubalantar nadin  sabon sarki Ahmed Nuhu Bamalli a matayin Sarkin Zazzau.

Shi dai Alhaji Bashari Aminu Iyan Zazzau yana daga cikin wadanda suka yi zawarcin  nemi  sarautar ta Zazzau.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!