Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Sassaucin da JAMB keyi ga ƴan Arewa yasa sun zama malalata- El-Rufa’i

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai ya yi kira ga hukumar shirya jarabawa ta JAMB, da su daina bawa ƴan Arewa fifikon maki.

Gwamnan yace tun bayan samun ƴan cin kai dai, Arewa ce koma baya a bangaren ilimi, haka kuma bada fifikon maki ga su daliban na arewa baya kara musu komai face lalaci.

Gwamnan yayi wannan kira ne a jiya litinin, yayin wata tattaunawa da akayi da shi a gidan talabijin na Channels.

El¬-Rufai ya ce ya kamata ace ana bawa yan arewa maki kamar yadda ake bawa sauran dalibai daga kudan cin kasar nan, domin hakan zai kara musu kwazo matuka.

A kwana kwanan nan ne dai hukumar ta bayyana cewa ta rushe tsaida makin da ya kamata dalibai su zo dashi, sai dai a yanzu ta dora alhakin yin hakan akan su kansu jamio’i da su sanya makin da suka ga ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!