Labarai
SERAP ta buƙaci shugaba Tinubu ya bai wa Wike umarnin janye barazanar rufe ofisoshin jakadanci

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci, ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya bai wa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike umarnin janye barazanar da ya yi na rufe ofisoshin jakadancin ƙasashen waje 34 a Abuja.
Martanin ƙungiyar na zuwa ne bayan da hukumar kula da babban birnin tarayya FCTA, ta ce ana bin aƙalla ofisoshin jakadanci 34 kuɗin haya tun 2014.
Ofisoshin jakadanci da abin ya shafa sun haɗa da na Ghana, Thailand, Equatorial Guinea, Côte d’Ivoire, Rasha, Philippines, Netherlands, Turkiyya da Guinea, Ireland, Uganda, Iraqi, Zambiya, Tanzaniya, Jamus, Kongo, Venezuela da Koriya da Trinidad da kuma Tobago.
Sauran sun haɗa da Masar, Chadi, Indiya, Sudan, Kenya, Zimbabwe, Ethiopia, Indonesiya da Tarayyar Turai da Switzerland da Saudiyya da China da kuma Afirka ta Kudu.
Wata sanarwa da SERAP ta fitar a shafinta na X ranar Litinin, ta yi gargaɗin cewa barin Wike ya ɗauki matakin zai saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjeniyoyin hulɗar diflomasiyya.
You must be logged in to post a comment Login