Connect with us

Labarai

Shahararriyar mawaƙiyar Hausa Magajiya Ɗanbatta ta rasu

Published

on

Shahararriyar mawakiyar Hausa anan Kano Magajiya Ɗambatta ta rasu.

Mawaƙiyar ta rasu bayan gajeriyar rashin lafiya a gidanta da ke Ɗambatta a yammacin ranar Juma’a.

Magajiya Ɗanbatta ta rasu tana da shekaru 86.

Tsohuwar mawaƙiyar na da lalurar gani wanda hakan yasa ta yi rayuwar ƙunci.

A watan Disambar 2018, Babban Editan Jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar ya ƙaddamar da wani asusun tallafa mata, inda ta samu sama da Naira miliyan 5 a cikin asusun.

Wanda da shi ne aka yi amfani wajen gina mata gida madaidaici da kuma kula da rayuwarta.

Magajiya Ɗambatta, ɗaya ce daga cikin mawakan Hausa da ta shahara a shekarun 1970 zuwa 1980.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!