Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan ya rasu

Published

on

Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan ya rasu.

Rahotanni daga iyalan Marigayin sun bayyana cewa ya rasu da safiyar yau Juma’a bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

An haifi Alhaji Mukhtar Adnan a shekarar 1926 kuma tsohon sarkin Kano Sir Muhammad Sanusi ne ya naɗa shi a matsayin sarkin Bai a shekarar 1954 domin ya gaji mahaifinsa Sabon Dambazau.

Marigayi Sarkin Bai shi ne kwamishinan ilimi na farko a jihar Kano a 1968, kuma halarci makarantar Elementary da ke Ɗanbatta da makarantar Midil ta Kano da kuma makarantar malamai a garin Zaria.

Jama’ar Musulmi na alhinin rashin Malam Mas’ud Hotoro

Marigayin ya kasance tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya a jamhuriya ta farko, kuma guda daga cikin mamba mafi daɗewa a majalisar masarautar Kano masu zaɓen sarki tsawon shekaru 63.

Kuma yana cikin waɗanda suka zaɓi  sarakuna da suka haɗar da Sarkin Kano Muhammadu Inuwa a 1963, Sarkin Kano Ado Bayero 1963 zuwa 2014, sai Sarkin Kano Muhammad Sanusi 2014 da Sarkin Kano Aminu Bayero a 2020.

Za a yi jana’izar sa a garin Ɗanbatta bayan saukowa daga masallacin Juma’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!