Labarai
Shalkwatar tsaro na shirin gurfanar da wadanda ake zargi da yukurin juyin Mulki

Shalkwatar tsaron Najeriya, ta ce, ta kammala binciken da ta ke yi kan yunƙurin kifar da gwamnati wanda aka yi a shekarar da ta gabata, inda ta ce, nan gaba kaɗan za ta gurfanar da jami’an da ta samu da hannu a lamarin a gaban kotun sojoji domin fuskantar shari’a.
Shalkwatar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, wanda wannan ne karo na farko da ta fito ta tabbatar da an yi yunƙurin juyin mulkin.
A cikin sanarwar, wadda mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce tuni rundunar tsaron ta miƙa rahoton bincike zuwa ga shugaban ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken ya gano tare da tabbatar da cewa wasu sojoji sun yi yunƙurin kifar da gwamnati, “sannan da sannu waɗanda aka gano sun aikata laifi za su bayyana a gaban kotun soji ta musamman domin fuskantar shari’a kamar yadda kundin tsarin soji ya tanada.
You must be logged in to post a comment Login