Labarai
Shalkwatar tsaron kasar nan ta karyata jita jitar juyin mulki

Shalkwatar ta karyata rahotannin da ke cewa an kama sama da jami’an soja goma sha biyu bisa yunkurin juyin mulki inda ta ce rahotannin da wasu kafafen yada labarai a kasar nan suka bayar kan wanna zargin labarin kanzon kurege ne.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai na shelkwatar tsaron kasar nan Tukur Gusau ya fitar, ta ce ikirarin da wasu kafafen yada labarai ke yi karya ce kawai.
Sanarwar ta ce tun a farkon wannan watan aka kama wasu jami’an soja 16 bisa laifin rashin ladabi da biyayya, amma hakan baida alaƙa da shirin juyin mulkin kamar yadda wasu ke yadawa.
You must be logged in to post a comment Login