Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shayar da nonon uwa na farkon mako babban rigakafi ne ga jarirai – Masani

Published

on

Wani masani a bangaren abinci mai gina jiki da kara lafiya kuma mataimakin darakta a hukumar lafiya matakin farko Malam Murtala Inuwa ya ce shayar da nonon uwa zalla na farko musamman mai kalar rawayar nan tsahon kwana bakwai shine babban rigakafi na farko da ke kare yaro daga kamuwa da cututtuka.

Malam Murtala ya bayyana hakan ne yayin taron yawar da kai da kungiyar Ma’aikatan bangaren abinci mai gina jiki ta kasa reshen jihar Kano ta shirya a kwalejin koyar da harkokin tsafta a yau.

“Malam Murtala ya kuma kara da cewar da yawan iyaye basu san ta yadda zasu shayar da ‘ya’yansu ba wanda hakan ke taka rawa wajan raunata lafiyar yaran”.

A nasa bangaren tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafizu Abbakar wanda guda ne daga cikin ‘ya yan kungiyar, cewa ya yi da yawan mutane basu san wadanne irin abinci ya kamata su ci don gina jikin su da kuma kare lafiyar su ba.

Dakta Bashir Bala Getso wanda shine Shugaban makarantar koyan aikin tsaftar ya ce “Yawaitar cututtuka da ake samu a yanzu na da nasaba da rashin cin abinci mai kara lafiya”

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta ruwaito cewar Auwal Musa wanda shine shugaban kungiyar dalibai dake karantar bangaren abinci mai gina jiki da kara lafiya, ya ce,‘Suna fuskantar kalubale kan yadda gwamnati bata baiwa bangaren nasu muhimmancin da ta kamata”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!