Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shehu Sani:Muna karbar naira miliyan goma sha uku da dubu dari biyar a kowanne wata

Published

on

Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a zauren majalisar kasar dattijai sanata Shehu Sani ya ce shi da sauran abokan aikin sa na karbar kimanin naira miliyan goma sha uku da dubu dari biyar a kowanne wata a matsayin kudaden tafiyar da al’amura na yau da kullum.

 

Cikin wata zantawa da manema labarai sanata Shehu sani ya ce ya ce kudaden tafiyar da al’amuran yau da kullum da suke kar ba ba su hadar da naira dubu dari bakwai na kudaden albashi da alawus din su da ake basu duk wata.

 

Ya ce ko da ya ke babu wasu bayanani da ke cewar kudaden ga dalilin bnayar da su, amma an dole ne ko wannen sanata ya bayar da shaidar bayanan kashe kudin na rasti bayan kashe su.

 

Haka kuma ya ce kudaden da ake baiwa kowanne sanata wajen gudanar da ayyuka a mazabar sa na daga cikin wadannan kudade

 

Sanatan ya ce ko da yake wadannan kudaden dole ne a kawo shaidar yadda aka batar da su, inda ya ce naira dubu dari bakwai da hamsi ne kawai ake baiwa sanatatocin su sha saha’anin gabansu batare da bada rasitri ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!