Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Shekaru 20 da rasuwar Malam Lawal Kalarawi: Ko yaya mutanan Kano ke  tunawa da shi?

Published

on

Malam Lawal Kalarawi shahararran Malamin Addinin musulunci ne da yayi shuhura a Kano da arewacin Najeriya sakamakon barkwanci da shehin Malamin yake yi idan yana gudanar da wa’azi na Addinin Musulunci.

Sheikh Lawan Kalarawi ya rasu a watan Disambar shekarar 1999 lokacin azumin watan Ramadan.

A watan da Disambar da muke ciki na shekarar 2019 Malam Lawan Kalarawi shekarar sa ashirin cif kenan da rasuwa.

A lokacin da Malam Lawal Kalarawi yake raye al’umma da dama na son sauraran wa’azinsa , hakan ba zai rasa alaka da barkwanci da Malamin yake da shi ba lokacin da yake gudanar da Da’awar Musulunci.

Shuhurar da Malam Lawan Kalarawi yayi a guraran da yake wa’azi musamman a filin Shahuci dake tsakiyar birnin Kano ta saka ake cika makil domin sauraran wa’azin Marigayi Malam Lawan Kalarawi.

Wasu na alakanta barkwanci da Marigayi Shehin Malamin ke yi a matsayin dabara ta jawo hankalin mai zuwa wa’azi.

Kamar yadda addinin Musulunci ya bukaci masu kira zuwa ga kalmar Allah da su zama masu dabara wajen yin Da’awah da kira ga hanyar Allah cikin sauki, ya saka Malamin Addinin musuluncin ke jan hankalin masu sauraran sa da barkwanci da dabaru.

Lokacin da Malam Lawan Kalarawi ke raye yana amfani da guraran da yake wa’azi domin gayawa mahukunta gaskiya musamman ma ta hanyar barkwanci.

A lokacin gwamnatocin mulkin Soja an daure Malam Lawal Kalarawi sakamakon yadda yake fadin gaskiya a guraren da yake  wa’azi.

Daga cikin wadanda Marigayi Malam Lawal Kalarawi ya koyar akwai daya daga cikin shahararrun Malamin Addinin Musulunci da ke nan Jahar Kano , wato sheikh Tijjani Bala Kalarawi .

Kafin rasuwar Malam Lawal Kalarawi a watan Disambar shekarar 1999 lokacin da al’ummar musulmin Duniya ke gudanar da azumin watan Ramadan  ya zagaya sassa daban daban na wajen birnin Kano domin gudanar da wa’azi.

Malam Lawal Kalarawi ya ziyarci wajen birnin na Kano kai kace bankwana yake da al’ummar Jahar Kano a ragowar shekarun da suka rage masa a Duniya.

Unguwannin wajen birnin Kano da Marigayi Shehin Malamin ya rika ziyarta Tarihi ya nuna cewa bai taba zuwa unguwannin ba domin gudanar da wa’azi.

Unguwar da wannan marubuci ba zai manta ba da Malam Lawal Kalarawi ya ziyarta itace unguwar Badawa dake yankin karamar hukumar Nassarawa.

Malam Lawan Kalarawi ya kai kimanin fiye da sati biyu a shekarar 1996 , shekaru uku kafin rasuwar sa yana gudanar da wa’azi a wani shahararran fili da ake kira filin Joni dake unguwar Badawa a karamar hukumar ta Nassarawa .

Malamin yana halattar wannan guri ne da misalin karfe 10 zuwa 10:30 na dare domin fara wa’azi.

Amma kafin isowar sa wasu daga cikin mukarraban sa da suka hada da Malam Usman da Malam Idi na fara yin sharar fagge a wannan fili na Joni da Malam Lawal Kalarawi ke gudanar da wa’aazi.

Da zarar shehin Malamin ya bayyana a gurin za’a dakatar da komai , shi kuma zai shiga tsakiyar Malam Idi da wani maja bakinsa , nan take Malam Lawal Kalarawi zai fara gudanar da wa’azi.

Shehin Malamin ba ya barin filin Joni dake Badawa sai kusan karfe biyu na dare.

A lokacin ne yake cewa mutanan Badawa yana gode mu su kwarai da gaske sakamakon karrama shi da suke yi da samfurin lemon TEEM.

Daga cikin barkwancin da shehin Malamin ya rika yi shi ne yakan ce idan ya gama da Badawa al’ummar yankin Jogana ma na neman sa , amma yakan gayawa mahallatta wa’azin cewa shi baya ganin zai je Jogana saboda kar su tare shi da kunun zaki, tunda mutanan Badawa sukan ba shi lemon Teem.

Malam Lawal Kalarawi ya sha fada a wa’azin sa kafin ya koma ga mahallincin sa ta hanyar barkwanci cewa ranar da ya rasu mala’iku za su yi masa barka da zuwa inda za su ce Kalarawi yaushe ka zo , shi kuma za ice jiya nazo da daddare.

A ikon a Allah kalarawi ya rasu  goshin magariba wanda ba’a  gudanar da jana’izar sa ba sai washe gari.

Daya daga cikin shaharrun malaman addinin Musulunci da suka rayu a Jihar Kano, Marigayi Sheikh Aminuddin Abubakar bayan kammala Sallar  Tarawihi a masallacin sa dake unguwar Suleiman Crescent yace Malam Lawan Kalarawi shi ne Malamin da ya fara fadar gaskiya a Kano a cikin wa’azin sa da yake gudanarwa.

A cikin shekaru 20 da Malam Lawal Kalarawi yayi a iya cewa ta wadanne hanyoyi al’ummar Jahar Kano ke iya tunawa da Marigayi Malam Lawal Kalarawi.

Al’ummar Musulimi da dama na alhinin rashin Malam Lawal Kalarawi musamman ma  salon da yake amfani da shin na gudanar da wa’azi.

Marigayi Malam Lawal Kalarawi ya rasu ya bayar ‘Ya daya tal da jikoki.

Da fatan Allah madaukakin sarki yayi masa rahama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!