Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shekaru na suna buƙatar hutu – Buhari

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce yana sa ran barin ofishinsa a daidai lokacin da shekarun sa ke buƙatar hutu, daga yin aiki tsawon awanni a kowacce rana.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na ƙasa NTA a jiya Alhamis.

Shugaban ya ce da yawa daga cikin takwarorinsa na jin dadin ritayar da suka yi, kuma yana fatan ya yi koyi da su nan da watanni 17 masu zuwa, lokacin da wa’adinsa na mulki ya ƙare.

A cewarsa tuni shekarun sa suka nuna masa cewa yin aiki a yanzu na tsawon awanni 6 zuwa zuwa 8 a rana, ba abin wasa bane.

Shugaba Buhari ya kuma ce ba ya tsammanin ‘yan Najeriya za su yaba masa idan ya bar mulki, sai dai kawai su gane cewa ya yi iya ƙoƙarinsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!