Labarai
Shettima zai wakilci shugaba Tinubu a taron majalisar dinkin duniya

Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, zai wakilci Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 da za a gudanar a New York daga gobe Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28 ga Satumban bana.
Mai bai wa mataimakin shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha, ya ce Shettima zai halarci taron tunawa da cikar Majalisar Dinkin Duniya shekaru 80, tare da shiga tattaunawar manyan shugabannin duniya.
A ranar Laraba 24 ga Satumba, Mataimakin Shugaban ƙasan zai gabatar da jawabin Najeriya a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, sannan ya halarci taron sauyin yanayi da Majalisar ta shirya, inda Najeriya za ta sanar da sabbin matakan kare muhalli karkashin yarjejeniyar Paris.
Shettima zai kuma shiga taron koli kan samar da gidaje masu araha da shugaban Kenya zai jagoranta, kafin ya wuce birnin Frankfurt da ke ƙasar Jamus don ganawa da jami’an bankin Deutche kafin dawowa gida Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login