Labarai
Shirin ACRESAL na Kano ya ƙaryata zarge-zargen da aka yi masa

Shirin daƙile matsalar ƙafar Ruwa da matsalolin sauyin yanayi musamman a wuraren tsandauri ACReSAL na Kano, ya yi watsi da wani faifan bidiyo da ya karaɗa shafukan sada zumunta wanda ke zargin shirin da rashin gudanar da aiki yadda ya dace a fadin jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da jami’ar sadarwa ta shirin Maryam Abdulqadir ta fitar a yau Asabar, shirin na ACReSAL, ya bayyana bidiyon a matsayin wani yunkuri na bata wa shirin suna.
Fitar da wannan sanarwa ya biyo bayan tambayoyi da dama daga ‘yan jarida masu neman ji daga bakin mahukuntan shirin domin samun sahihan bayanai.
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa, ana aiwatar da shirin na ACRESAL ne a karkashin wata yarjejeniya da ta kunshi gwamnatin tarayyar da jihohin Arewa 19 da birnin tarayya Abuja da kuma bankin duniya.
Jami’ar ta cikin sanarwar ta ƙara da cewa, sanin kowa ne shirin na ACReSAL ya gudanar da dimbin ayyuka da dama a jihar Kano kuma a yanzu haka ma akwai aikace-aikace da dama da suke gudanarwa
Ana gudanar da ayyukan wannan shirin ne da mahimman takardu kamar Littafin Aiwatar da Aikin watau (PIM) da Takardun tasawirar Aikin (PAD,) waɗanda ke ɗauke da manufofi da ƙa’idodin aiki masu mahimmanci don cimma maƙasudin ci gaban Ayyukan shirin (PDO).
Bugu da ƙari, an tsara aikin ACReSAL don yin aiki a cikin iyakokin tsarin PDO na tsawon shekaru shida.
Dukkan ayyukan dole ne a samo su daga Tsare-tsaren aiki na shekara-shekara da Shirye-shiryen kashe kudade da sashen gudanar da ayyukan jiha (SPMU), tare da haɗin gwiwar ma’aikatu, sassan da hukumomin da suka dace (MDAs), wanda Ma’aikatar Muhalli ta Jiha ta amince da shi, kuma Bankin Duniya shi ma ya amince da shi.
Tun lokacin da aka kafa shi, aikin Kano-ACReSAL ya sami gagarumar nasara a sassansa.
Faifan bidiyon da aka yaɗa ɗin ya yi zarge-zarge guda uku: Kano-ACRESAL tana haƙa famfunan hannu maimakon rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, wadanda suka ci gajiyar Asusun Tallafa wa al’umma (CRF) na kirkire-kirkire ne, da kuma cewa ba a taɓa siyan na’urori da kuma manyan motocin daukar kaya domin kwashe shara ba.
You must be logged in to post a comment Login