Labaran Kano
Shirin Bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano zai fara Bayen Shanu
Shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano , Kano state Agro Pastoral Development Project KSADP, zai fara shirin Bayen Shanu don bunkasa yawaitar Madara a jiha.
Shugaban shirin Malam Ibrahim Garba , ne ya bayyana haka , inda ya ce shirye shirye sunyi nisa wanda ake sa ran fara gudanarwa a cikin shekara mai kamawa a Kadawa dake Karamar hukumar Garun Malam.
Malam Ibrahim Garba Muhammad, ya yi jawabin ne a Ya yin da ya karbi kungiyar Bunkasa al’adun Fulani da cigaban su ta kasa Fulbe Development and Cultural Organization ,FUDECO a lokacin kawo ziyara ofishin hukumar karkashin jagorancin shugaban su na jiha Abdullahi Isa.
Labarai masu Alaka.
Gwamnatin jihar Kano zata bada hayar Kadada 1,000 don noman Kasuwanci
Shirin bunkasa noma da kiwo na jiha zai hada kai da cibiyoyin bincike
Muhammad Garba , ya ce “Shirin zai taimaka wajen bunkasawa tare da habbaka tattalin arzikin makiyaya wanda yanzu basa iya samar da abinda ya Gaza lita 1, wanda da zarar anyi Bayen Shanun zasu iya samar da lita 15″.
Babban Jami’in ya kuma ce shirin ya kammala tsari na saka hannun jari wajen bunkasa noman ciyawar Shanu da gurin kiwo a Dajin Dansoshiya don samar da kasuwanci ga makiyaya tare takaita yawon na makiyaya a fadin kasa.
Bugu da kari jami’in yace za ‘a fara allurar rigakafin Dabbobi a nan da makwanni masu zuwa, kana ya bukaci hadin kan kungiyar ta FUDECO don wayar da kan Fulani Makiyaya kan tsarin don su ci moriyar sa.
Da yake nashi jawabin shugaban na FUDECO ,Abdullahi Isa kamar yadda Kakakin shirin Aminu Kabir Yassar , ya ruwaito a takardar da ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai , ya ce kungiyar su ,kungiya ce mai zaman kanta wato NGO, wacce ta dau gabar shawo kan matsalolin da Fulani ke fuskanta.
” Munzo ne don ganin wannan sabon tsarin tare da duba yiwuwar shigar mu cikin sa don samun bunkasa tattalin Arzikin Al’ummar mu” inji shugaban.
You must be logged in to post a comment Login