Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Shirin bunkasa noma zai hada kai da cibiyar NAPRI don samar da abincin dabbobi

Published

on

 

Shirin bunkasa noma da kiwo na jihar Kano, Kano state Agro Pastoral Development Project ,KSDAP, zai hada kai da cibiyar bunkasa samar da dabbobi da binciken su ta kasa National Animal Production Research Institute , NAPRI , dake jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria akan samar da noman ciyawar shanu a Kano.

Kwararren jami’in shirin akan kiwon dabbobi nau’in tsuntsaye Dakta Garba Saleh , ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara ga shugaban cibiyar binciken Farfesa Abdullahi Muhammad , inda ya ce shirin yana matukar bukatar taimakon cibiyar wajen samar da iri da bunkasa shi don samar da wadatattun Dabbobi.

Jami’in ya kara dacewa mun fuskanci cewar samar da tsarin wadatattun dabbobi mai dorewa na fuskantar tasgaro sakamakon rashin tsarin samar da noman abincin su , don haka akwai bukatar samar da wadataccen abincin.

Labarai masu Alaka.

Gwamnatin Kano zata zaunar da makiyaya guri daya

Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai fara yiwa dabbobi Allura ta Rigakafi

Dakta Garba Saleh , ya ce samar da noman ciyawar da irinta zai tabbatar da karuwar madara mai inganci tare da rage yawan kashe kudade ga makiyaya , kuma hakan zai zaunar da makiyaya guri daya tare da kare su daga yawan fadace fadace da Manoma da barayin Shanu.

Ya kuma kara dacewa shirin zai inganta tare da samar da kamfani masu zaman kansu don shiga cikin tsarin tare da kasuwancin sakamakon ribar da za’a samu a cikin noman.

Dakta Garba Saleh, ya ce shirin zai maida hankali akan kananan manoman ciyawar musamman ma wanda suke a guraren da suke da yalwar samar da ita.

Inda ya ce zuwa yanzu haka sun kammala shiri don samar da iri uku na bunkasa samar da madarar , da suka hada da ,’Stylo da ciyawar Nappier sai Gamba’, don haka shirin yake bukatar hadin kan cibiyar don samar da abinda ya kamata akan bunkasa shirin tare da samun nasarar sa.

A nasa jawabin shugaban cibiyar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Muhammad, Kumar yadda kakakin shirin Aminu Kabir Yassar , ya ruwaito a takarda mai dauke da sa hannun sa , yace cibiyar a shirye take a koda yaushe don samar da duk abinda aka nema , tare da bada shawarwari da kayan aiki da zata iya samarwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!