Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Legas ta koka kan yawan samun masu Corona a jihar a kullum

Published

on

Gwamnatin jihar Lagos ta ce akwai mutane akalla dubu biyu da dari da casa’in da ake jiran su mika kansu ga cibiyoyin killace masu fama da cutar a jihar domin fara basu kulawar da ta dace.

Kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a, yana mai cewa matukar jihar na son kawo karshen yaduwar cutar ya zama lallai mutane su ci gaba da mutunta dokar yin amfani da takunkumin rufe baki da hanci da kuma bada tazarar mu’amala a tsakanin juna da yawaita wanke hannu.

Ta cikin sanarawar da Abayomi ya wallafa a shafin sa na Twitter ya bayyana damuwar sa kan yadda a kullum ake samun adadi mafi yawa na wadanda ke kamuwa da cutar a jihar.

Akin ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu a yiwa mutane dubu arba’in da biyar da dari hudu da chasa’in gwajin cutar a jihar.

Akin Abayomi ya kuma ce wadanda jihar ta samu masu dauke da cutar sun kai dubu sha daya da dari biyar da tallatin da bakwai, yayin da wadanda ke cibiyar killace masu cutar yawan su ya kai dubu biyu da dari daya da casa’in da daya yayin da jihar ta sallami a kalla mutane dubu daya da dari bakwai da hamsin da uku.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!